Kwakwumeti
Ummi Tee @Ummitunau
Yara na marmarin Shi sosai shiyasa na gwada musu kuma sunyi ta Santi 😋
Kwakwumeti
Yara na marmarin Shi sosai shiyasa na gwada musu kuma sunyi ta Santi 😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fasa kwakwa sai ki yanka ta
- 2
Sannan ki wanke ta da kyau
- 3
Kisa magogi(grater) ki goga amma manya yafi kyau
- 4
Sai ki auna kofi daya
- 5
Sai ki zuba rabin kofi na suga ciki sannan ki motsa da kyau
- 6
Sai ki zuba mai ko buta cikin frying pan yayi zafi amma ba sosai ba
- 7
Se ki zuba kwakwar da kika sa ma suga kiyi ta motsawa da kyau
- 8
Baa barin motsawa kada ya kone yayi daci kisa wuta kadan
- 9
Idan kin kashe kada ki bar motsawa zata hade kiyi ta motsawa har ta huche
- 10
Sai ki samu mazubi ki zuba ki rufe
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16512970



sharhai (3)