Dankali, kwai, plantain Hadi da kaza

#Lunchbox oga yakanso yaje office da wannan hadin, to nakanyishi baki daya tare dana 'yan makaranta.
Dankali, kwai, plantain Hadi da kaza
#Lunchbox oga yakanso yaje office da wannan hadin, to nakanyishi baki daya tare dana 'yan makaranta.
Umarnin dafa abinci
- 1
Zakiyi amfani da dankali madaidaita, sai a Yankee bawon, sannan axo ayankashi da dan girma, akawo man gyada a Dora a wuta, akawo Dan albasa a jefa aciki, idan albasar tataso sama, alaman man yayi zafi, sai kiwanke dankalinki, kikawo gishiri kibarbada yadda kikeso, sai kixuba acikin man, ba',acika motsawaba, idan ya soyu zai taso sama, sauki kwashe a Wani wurin
- 2
Dana kwashe dankalin, na yayyanka, plantain din na barbada gishiri, sannnan nasoya acikin Mai din, da yayi nakwashe.
- 3
Na zuba man kadan a Wani kasko, nafasa kwaina nakawo albasa, Koren tattasai da ja nazuba aciki na barbada maggi da dan gishiri sannan nakada nasoya, da yayi nakwashe
- 4
Naman kazar idan gobe zakayi amfani dashi sai acire bangaren da kakeso na kazar sai a barbadeshi da sinadaran dandano asashi a fridge a barshi yakwana har dandano ya hade a jikinshi, sai a dauko asa a fryer(abungashi).
Similar Recipes
More Recipes



sharhai (4)