Jollof din taliyar hausa da indomie
inada wata sauran taliyar hausa yar kadan tafi wata uku a ajiye na kasa amfani da ita sabida tayi kadan da sauran kifi na soyayye guda 1 satinsa daya a fridge sai na dauko su na hada da indomie na dafa su tare a wannan gasa ta tsoho ya tadda sabo ya kuma yi dadi sosai #omn

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na gyara kayan miya na wanke na jajjagasu na dora tukunya a wuta na saka mangyada kadan na juye jajjagen na soya shi samasama sai na kawo ruwa kopi 2 na zuba na saka maggi daya da maggin cikin indomi dn.
- 2
Na dauko kifi na saka ya dan tafasa sai na fara zuba taliyar hausa sai na saka indomi dn ma na juya su na rupe na yan mintuna bayan yayi na yanka albasa na zuba akai na rupe ta dan turara shikenan
Similar Recipes
More Recipes

sharhai