Catfish pepper soup

Yana daya daga cikin kifin danake so gaskiya sai dai yarana Basu damu dashi
Catfish pepper soup
Yana daya daga cikin kifin danake so gaskiya sai dai yarana Basu damu dashi
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki gyara kayan miyarki ki jajjagasu sannan ki saka mai kadan a tukunyarki sai ki zuba kayan miyarki aciki ki soya sannan ki dauko ginger da garlic da kika gyara ki zuba sai maggi and species dinki ki zuba suma
- 2
Sannan ki daidaita ruwa akai yadda zai dafa Miki kifin kar a saka ruwan da yawa saboda kifin bashi da wahalan dahuwa sai ki rufe ya tagasa
- 3
Sai ki dauko kifin shi kuma ki gyara ki wanke yadda karnin zai fita Zaki iya saka kanwa ko lemon tsami ko vinegar wajen wankewa Yana dauki karnin
- 4
Sai ki dawo wajen tukunyarki sannan ya tafasa sai ki zuba kifinki ki barshi yayi Kamar 10 to 15 min sai ki sauke
Similar Recipes
More Recipes






sharhai (2)