Soyayyar taliya

Hauwa Rilwan @hauwaskitchen
Kwana biyu banyi posting ba😅yanzu kam na dawo da qarfina inshaAllah
Soyayyar taliya
Kwana biyu banyi posting ba😅yanzu kam na dawo da qarfina inshaAllah
Umarnin dafa abinci
- 1
Doru tukunya da ruwa a wuta ki zuba gishiri da curry in sun tafasa ki karya taliya ki zuba a ciki ki dafa taliyar tsawon minti biyar
- 2
Idan ta tafasa ki tsane ki barta ta huce har ruwa ya fita duka
- 3
Ki fasa kwai ki soya ki dagargaza shi (scrambled)
- 4
Ki dora pan a wuta ki saka mai ki zuba ginger and garlic paste ki sa jajjagen tarugu da tattasai da albasa ki soya
- 5
Ki kawo nama ki yanka shi kanana ki zuba a ciki
- 6
Ki kawo taliyar da kika tsane ki zuba a ciki ki jujjuya ki zuba dandano
- 7
Ki kawo kwan da kika soya ki zube a ciki ki cigaba da juyawa tsawon minti biyar
- 8
Taliya ta kammala na hada ta awara me kwai
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16819863




sharhai