Kulele da Mai da yaji

Assalamu Alaikum insha Allah zagabatar makuda kulele ,kulele Wani local food ne da akeyi akatsina Abincine na gargajiya anayin amfani da wake da yaudo karkashi da kanwa sannan ana amfani da ganyan kalgo awajanyinsa kaman yanada kukasan wasu jahohi sunayin tubani to akatsina anayin kulele

Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko Zaki tanadi kayan Dana lussafa ki surfa wake ki wanke ki ajiye waje guda kaman haka
- 2
Sannan ki markada shi da ruwa kada yakai na kosai nikuwa kizuba gishiri da yaudo ki da kanwa ki juya kaman haka
- 3
Sannan ki wanke ganyan kalgo ki ajiye waje guda ko kitchen paper ko takadda inda kargo Zaki sai kidinga diban kullun ki zuba acikin ganyan kalgo din kina mannewa kinasawa Atukunyar dambu inkuma takadda ne sai ki shefeta da.mai sai kidinga zuba kaman haka kina nadewa
- 4
Sannan kijera Atukunyar dambu kirufe da leda ki turarashi kaman haka
- 5
Daya daho zakifara jinyana kamshi
- 6
Kunga yadda yakeyi zakiga yayi Saka Masha Allah
- 7
Sannan abanbare sa Mai da yaji da maggi kaman haka
- 8
Allah ya amintar da hannayenmu nagode Aci lafiya
Similar Recipes
More Recipes

sharhai