Dafadukan shinkafa da alale
😋😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki gyara kayan miyar ki bayan kin gyara ki jajaga su sai ki daura mai a tukunya idan yayi zafi ki zuba cefanan ki soya shi bayan nan sai ki zuba ruwa ki barshi ya tafasa ki zuba su maggi da gishiri sai ki barshi ya tafasa
- 2
Idan ya tafaso sai ki wanke shinkafa ki zuba ki rufe zuwa minti 30 idan ta fara tsanewa sai ki saka corry ki rufe ki barta da ita datsewa
- 3
Alalen kuma zaki gyara wanken ki sai ki zuba attaruhu da albasa da yar tafarnuwa ki bada akai maki markade idan an kawo sai ki zuba maggi da salt ki motsa kisa corry ki motsa sai ki samu leda ki kulla kisa cikin ruwa ki daura ki barta taita dahuwa kamar minti30 sai ki duba idan tayi sai ki Sauke
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8953923




sharhai