Dan wake
#Dan-wakecontest Dan wake yana daya daga cikin abincin gargajiya na hausawa, Akwai dan waken rogo akwai na fulawa wasuma har na semovita sunayi, Amma ni nafisan dan waken fulawa saboda yafi laushi da dadi. Yara da manya duk suna son dan wake saboda abun marmari ne. Ina matukar son danwake musamman inyaji yaji da kayan hadi, ina san cin danwake musamman in nasan zan fita sbd yana da rike ciki,sai mutum ya dade beji yunwa ba.

Umarnin dafa abinci
- 1
A zuba fulawa a kwano,a dauko kuka a zuba a kan fulawa a juya ya hadu
- 2
A dauko kanwa a zuba a kwano a zuba ruwa madaidaici ta jiku
- 3
A dauko ruwan kanwa a zuba a cikin fulawa a juya har sai ya hadu,amma a kula kar yayi ruwa kuma kar yayi tauri dayawa
- 4
A zuba ruwa a tukunya a daura a kan huta har sai ya tafasa
- 5
In ruwa ya tafasa, a dauko kwabin danwake da cokali.A ringa diban kwabin da cokali ana zubawa a cikin tafasheshen ruwa ana tsoma cokali a ruwan sanyi ana diban kwabin har sai ya kare
- 6
In an gama jefa danwaken a rufe tukunya a barshi ya dafu minti 15-20
- 7
In ya dafu, a debo ruwan sanyi a kwano,ana kwashe dan wake ana zubawa a cikin ruwan #no8
- 8
A bude tukunya a dauko guda daya a duba in ya dafu #no7
- 9
A dafa kwai, a wanke albasa, tumatir, koren tattasai da kabeji
- 10
A yayyanka kabeji,tumatir,albasa,koran tattasai da kwai
- 11
A zuba manja a abun suya a yanka albasa a ciki a soya
- 12
Dan wake ya kammala, A zuba danwake a mazubi
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (3)