
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fara jika cous cous din ki da ruwan dumi ki zuba mai aciki kisa cokali mai yatsu ki juya sai ki rufe shi sosai
- 2
Ki soya kayan miya tareda nama da kayan kamshi
- 3
Sai ki zuba ruwan da kika tafasa nama dasu,ki juye wannan ruwa acikin cous cous din da kika jika sai ki barshi minti biyu ya tsane sai ki sauke.
- 4
Sai ki zuba kayan miyan ki da kika soya da nama sai ki juya.Idan kinada buqata kina iya saka kabeji karas da koren wake. Aci dadi lafiya
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/9508745



sharhai (2)