Sakwara (pounded yam)

Sakwara tayi a rayuwa amma aikinta akwai wahala. Megida har gori yakemin wai kila nan iya bane shiyasa ban yi sai dai once a while kannen suyi Niko nace zan nuna mishi na iya amma Gaskiya na sani but its worth it ba laifi. @mrsjikanyari01 @Sams_Kitchen @Sams_Kitchen duk Ina gayyatanku. Ku taho mana da abin korawa 😂

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki samo doyarki mai kyau, ma daidaici
- 2
Sai ki fere ki wanketa da kyau
- 3
Sai ki zuba a tukunya da ruwa ma daidaici yadda zata dafata harta dan rage idan ta nuna
- 4
Sai ki zuba dan suganki wassu kuma gishiri suke sawa. Ki rufe kisa a wuta har sai ta dahu sosai
- 5
Saiki sauke ta. Gatanan kingani da dan ruwa ruwa aciki
- 6
Sai ki fara zuba doyarki a turmi ki fara dakawa kamar haka
- 7
Wannan dan ruwan da kika bari a tukunyan nan zakina zubawa akan doyan a yayinda ta fara laushi kamar haka
- 8
Kinga yadda ya kasance tayi laushi sosai ba laifi Amma
Zakisha daku kam ki iso wannan gurin. Gashi tayi da ko yadda ake bukata - 9
Kindai gani yadda nawa tayi laushi tayi danko ga harke kuma tayi laushi sosai ba guda guda aciki. Toh shi ake kira da sakwara
- 10
Shikenan saiki fara daurawa a leda da sauri kar tayi sanyi
- 11
Naci nawa da miyar agushi
- 12
Hmmmmmmm dadi ba a magana saida wadda yaci. Nikam na kusan cinye leda daya ba Miya tsabar yadda tayi yadda akeson
- 13
Kunga na huta da gorin oga lols 😂
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (10)