Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko a zaa barzo shinkafa sai a tankade a cire garin sai ayi amfani da tsakin. A wanke tsakin a barshi ya tsane sai a zuba ruwa a madambaci a dora yayi yan mintuna sai a sauke.
- 2
A samu abu a juye dambun sai a zuba gyada,mai,albasa,tarugu,sinadarin dandano, zogale da kayan kamshi. Sai a jujjuya a maida akan wuta idan yayi zakiji yana qamshi sosai. Zaa iyaci a haka ko da miya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10481231



sharhai