Wainar filawa
Tana da dadi musamman Tasha atturuhu da albasa
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki tankade filawa ki zuba ruwa ki Sami ludayi ki damata kar tayi ruwa sosai Kuma kar tayi kauri
- 2
Ki jajjagaggen attaruhunki,ki yanka albasa kanana ki zuba akan kwabin filawar
- 3
Ki bare Maggi da gishiri ki zuba,Amma Ni banyi amfani da gishiri ba.
- 4
Ki Dora kasko a wuta ki zuba Mai kadan kina dauko kwabin filawarki da ludayi kina zubawa a kaskon,in kasan ya soyu saiki juya haka zakinayi har ki gama.
- 5
Anayi wainar filawa da man gyada ko manja,ana Kuma cin ta da yajin barkono
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16053630




sharhai