Soyayyen kifi (Mackerel)

Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Soyayyen kifi batareda ya pashe ko ya watsa ba cikin sauki #dandano
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki yanka kifinki ki wanke shi tass
- 2
Sannan ki tsame ruwa ki saka a rariya
- 3
Ki cire wannan lakkar nide bani sonta inda kwan kifi ne da na barshi 😉
- 4
Se ki zuba gishiri cikin filawa ki motsa zaki iya saka magi fari ko cube idan kina so nide gishiri kada nasaka se ki jefa kifin ki zakuda yadda kike gani a video
- 5
Idan ko ina ya samu se ki aza mai bisa wuta yayi zafi ssnnan ki raba shi 2 baa son ki zuba dayawa ze makale
- 6
Ki nayi kina juyawa har ya soyu
- 7
Kinga kifin ki gwanin ban shaawa ba ruwanki da fashewa
- 8
Zaki iya ci haka ko idan zaki saka cikin miya kin huta ko ki ci da garau garau
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16770079

















sharhai