Doughnut me adon icing siga

Akwai dadi sosai,kuma maganin kwadayi ne 😋😋😋
Doughnut me adon icing siga
Akwai dadi sosai,kuma maganin kwadayi ne 😋😋😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za'a tankade filawa a roba,a zuba siga da madarar gari a gauraya su.
- 2
Sai a zuba yis acikin ruwan dumi kopi daya a gauraya sai a zuba acikin wannan filawan ana gaurayawa har ya hade jikanshi,a gauraya kaman tsawon minti sha biyar,sai a dauka bota cokali ukun a saka aciki a gauraya su sosai shima har tsawon min sha biyar.
- 3
Sai a murza a fitar da shape din round a barbada filawa a tray sai a daura a kai, sai a rufe ko da leda ko kitchen towel a barshi ya tashi tsawon minti talatin,sai a saka yatsa a tsakiyan a fitar da rami a tsakiyan.
- 4
Sai a saka mai a wuta a rage wutan sosai idan mai yayi zafi sai a saka a cikin mai a soya.
- 5
(Kwalliyan) a zuba icing siga a roba,sai a saka madarar gari a gauraya su, sai a zuba ruwa kadan a gauraya,sai a zuba akan doughnut din a saka sprinkles a kai,shikenan aci lafiya 😋😋😋.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai