Faten Dankali
#kadunastate ...gwada wannan girki don jindadin iyalinki
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki fere dankali ki wanke ta,ki wanke tarugu,tattasai,albasa,ki bare tafarnuwa da citta ki hadesu waje guda ki jajjagasu.
- 2
Daura tukunya akan wuta ki zuba man gyada yadda kikeso in man yayi zafi sai ki dauko jajjagagen kayan miyanki saiki zuba ki soya su,ki zuba maggi guda 2 saiki zuba ruwa dai dai sannan ki zuba sauran maggi da Kayan kam shi sai ki zuba ferarren dankalin ki rufe yaita nuna Kina dubawa,idan dankalin ya kusa saiki saka busashen kifi ki a sama kidan barshi ya nuna kaman na minti 2,saiki sauke kiyi serving.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10145163






sharhai