Bredin alkama

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Alkama yana da amfani sosai ajiki kuma yanada dadi sosai zaki iya cin wannan bredin da duk miyar da kikeso nidai da ferfesun naman rago nayishi kuma yayi dadi sosai#BAKEBREAD

Bredin alkama

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

Alkama yana da amfani sosai ajiki kuma yanada dadi sosai zaki iya cin wannan bredin da duk miyar da kikeso nidai da ferfesun naman rago nayishi kuma yayi dadi sosai#BAKEBREAD

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1\4 madarar gari
  2. Butter chokali biyu
  3. 5Garin alkama kofi
  4. 1\3 sukari
  5. chokaliGishiri rabin
  6. Yeast chokali biyu
  7. Mangyada chokali daya
  8. r

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga kayakin da zanyi amfani dasu

  2. 2

    Dafarko zakisamo robarki mai kyau sai kizuba garin alkamar aciki sannan kizuba madara da gishiri tareda sugar da yeast sai kijujjuya sannan kizuba mai kisake jujjuya wa sai kizuba ruwan dumi ki kwabashi sosai amma kar kwabin yayiruwa kawabi dai zakiyi kamar yanda zakikwaba fulawa sai kizuba butter akai kisake kwabashi sosai har tsawon minti biyar sannan kirufeta ki ajiye zuwa minti goma ko shabiyar sbd yatashi

  3. 3

    Bayan yatashi sai kidaukoshi kikara bugashi dakyau sai kirabashi gida biyu amma dayan yafi girma sai kidauko baking pan dinki kishafa mata butter ko mai sai kidau wannan dayan da yafi girma kirabashi gida shida sai kidau daya kidan fadadashi sai kizuba chocolate syrup aciki sai ki mulmulashi sannan kisaka acikin pan din. Haka zakiyiwa sauranma. Bayan kingama sai kisake rufeta kibarta sbd takara tashi.

  4. 4

    Sai kidauko kashi dayan kirarrabashi sai kidau daya kimurzashi tayi fadi sannan kidauko wani dan roba kokuma faranti ko murfin kwalba bama. Sai kicire circle sannan kidaura pan a wuta idan yayi zafi sai kirage wutan sosai sannan kizuba butter dan kadan sai kidau daya kidaura akan pan din bayan minti daya zuwa biyu sai kijuye dayan bangaren shima yagasu idan yagama gasuwa sai kicireshi kisaka acikin kitchen towel kokuma cikin flakes sbd yakarayin laushi. Haka zakiyiwa duka har kigama

  5. 5

    Sai kidiba wanchan wanda kika ajiye ko yatashi. Sai kifasa kwai daya ki kadashi da kyau sai ki shashshafa akai sannan kisa a oven ki gasa. baya kingasa sai kicireshi yasaha iska sannan kisamo leda mai karfi irin wanda ake saka bredi aciki sai kisashi kidaure bakin saboda kar isaka yashiga

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes