Samosa
Kitchenhuntchallenge
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki zuba fulawa da corn fulawa, gishiri kadan ki kwaba su da ruwa ki hada dough saiki rufeshi da towel na Dan lokaci
- 2
Ki tafasa namanki ki ki saka Magi da kayan kamshi sai ki dakashi ki ki yanka albasa ki jajjaga attarugu kadan sai ki soyasu tare da nama
- 3
Sae ki dauko fulawarki ki Kara murzata sannan ki yi dough yadda kikeson girmanta saiki Dan murzaki kadan sannan ki hada guda 5 wuri daya ki murza su idan kika aza daya Zaki shafa Mai ki zuba garin fulawa sannan ki Dora wani don kar su hade wurin murzawa
- 4
In kika murza sannan ki gasa kadan sae ki rabashi gida 4 sai ki nadashi ki rinka zuba kayan hadikin ki kwaba fulawa kina shafa wa a karshen hadin saeki soya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10875551










sharhai