Dafadukan shinkafa da wake

Dayawa mutanen da ke son dafasuka sunfison ta shinkafa da wake saboda tafi gardi
Dafadukan shinkafa da wake
Dayawa mutanen da ke son dafasuka sunfison ta shinkafa da wake saboda tafi gardi
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki wanke tukunya ki aza ruwa idan sun tafasa sai ki gyara wakenki ki zuba ki barshi kamar 5mins Yana tafasa sannan ki wanke shinkafa ki zuba,Zaki barshi yayita tafasa kamar 10mins sannan ki zube a kwando ki wanke ki aje gefe ki rufe
- 2
Saiki gyara tattasai, Tarugu da albasa ki jajjagasu
- 3
Saiki dauko tukunya ki zuba Mai sannan ki zuba jajjagenki kidan soyashi sannan ki zuba ruwa yadda bazasuyi yawaba
- 4
Saiki sa maggi da gishiri da curry kibarahi ya tafasa sannan ki zuba shinkafa ki motsa sosai sannan ki rufe
- 5
Sai ki yanka cabbage idan ruwan yayi kasa sai ki zuba saman shinkafa ki rufe.Idan ta tsotse ruwanta saiki sauke
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai