Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko ki ji'ka couscous da ruwa yayi kamar minti talatin za ki ga ya shanye ruwan
- 2
Sai ki wanke attaruhu da albasa ki jajjaga su a turmi ko kuma ki blending dinsu,
- 3
Sai ki zuba a cikin couscous sannan ki ďauko maggi, curry da gishiri ki zuba,
- 4
Sai ki fasa 'kwai isashe a ciki ki juya da kyau, sai ki samu leda ki 'ku'kkula a ciki ki dafa kamar alale,
- 5
Idan ya dahu sai ki sauke ki ciccire a ledar sai ki yanyanka shi ki dinga tsomawa a cikin 'kwai kina soyawa a cikin man gyaďa.... 😘😘
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11094699




sharhai