Spring Rolls
Umarnin dafa abinci
- 1
- 2
Sai a hada kayan hadin cikin spring rolls din. A zuba mai kadan a kasko a sa yankakkiyar albasa mai lawashi a soya sama-sama sai a zuba cabbage da carrot a cigaba da soyawa a zuba sinadarin dandano da kayan kanshi dai-dai misali ana juyawa har su kayayyakin su soyu. A sauke a ajiye gefe.
- 3
Sai a dauko kwabin flour da akayi a gustura shi kanana. A murza shi yayi fadi da shape din circle, a ajiye shi gefe a kara murza wani curin a shafa mai a kanshi a barbada flour akai a dora akan na farko haka zai a jera daya kan daya. Bayan an gama sai a kara murza shi a fadada shi sosai.
- 4
A dora kasko sai a gasa flour a juya dayan gefen daga zarar kaskon yayi zafi sai a sauke yadda bazata kone ba. Sai a bare flour a rarraba ta.
- 5
Sai a kawo hadin cabbage da carrot ana zubawa akan gashashiyar flour a nade a manne gefen da ruwan flour a soya a mai me zafi.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes














sharhai