Yam Balls
Sabon Salo, Iftar Idea
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki samu doya ki yanka rabi ki fere ki dafa da gishiri kadan in ta dahu ki sauke ki barta ta huce sannan ki daka
- 2
Se ki nika tarugu albasa tafarnuwa ki soya da mai kadan kisaka dandano da kayan yaji inada sauran tafasashen naman kaza se na daka na saka aciki
- 3
Se ki hada su duka ki garwaye sosai in ya hadu se ki mulmula girman yadda kikeso ki kada kwan ki ciki roba kada ki sa komai aciki don ze tsinke
- 4
Idan zaki fara suyawa ki jefa cikin kwai sannan cikin golden morn sannan cikin mai me zafi ki dan barshi yafara soyuwa sannan ki fara juyawa
- 5
Wannan zeyi dadi lokachin iftar a watan alfarma watan Ramadan Allah ya nuna mana amin se kisamu kunun ki me zafi...
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11728825















sharhai