Miyan dambun nama
Umarnin dafa abinci
- 1
Idan kika zuba mai a tukunya sai kisa albasa a man idan yayi zafi sai ki zuba naman kiyi ta juya wa sai kisa mai gishiri, curry da maggi kadan sai kiyi ta juyawa yana soyuwa har sai yayi brown ya soyu naman ya rabu da man sai ki kwashe naman ki bar man
- 2
Daga nan sai ki zuba kayan miyan ki wato attaruhu, albasa da tattasai din da kika markada ki soya idan ya dako soyuwa sai kisa su peas din da carrot din dasu kayan dandane ki soya
- 3
Sai kisa ruwa kadan a ciki ki bar shi ya dahu sbda su peas din daga nan idan yayi kaman minti 2 Sai ki zuba naman a cikin ki rufe shi ki rage wutan ki barshi ya dahu na kaman 1-2mints Sai ki kashe wutan,,,,, zaki iya cin shi da shinkafa koh cous cous
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11767284




sharhai