Ganda me yaji

HALIMA MU'AZU aka Ummeetah @cook_12470582
Ganda me yaji
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki kankare Ganda ki wanke da kyau
- 2
Ki zuba a tukunya kisa ruwa kofi 1,kisa gishiri, ki yanka albasa, ki zuba kayan kamshi ki rufe ki bari ya tafasa na minti 20.
- 3
Ki tsame sai ki zubar da ruwan dan rage danko.
- 4
Sai ki jajjaga tarugu, tattasai da albasa, ki sa mai a tukunya ki soya manja ki zuba kayan miyan su soyu sama sama
- 5
Daganan sai a dauki dandano, da kayan kamshi da gishiri a zuba a kayan miyan a jiya da kau, se a zuba gandar, a juya sosai, se ya hade
- 6
Se a zuba ruwa kadan a juya a rufe se komai ya hade, a barshi na tsawon minti 5,shikenan an gama, aci dadi lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12088323



sharhai