Miyar dankali da kayan lambu

Miyar dankali da kayan lambu
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaki wanke kazanki,ki saka albasa,thyme,maggi,curry,ginger powder ki tafasa kazarki,bayan kin dafashi sai ki soya ki ajiye a gefe,ki yanka tattsai dogaye,koren tattsai mai dogaye zaki yanka shi,carrot ma haka zaki yanka dogaye.
- 2
Sai ki ajiye a gefe.Ki dauki albasa kiyi grating a grater,garlic ma haka zakiyi grating nashi sai ki daura tukunya a kan wuta ki zuba mai kafun ki zuba grated garlic da albasa da kikayi grating,ki zuba cumin,thyme,rosemary,curry,black pepper ki soya sosai kafun ki zuba jan tattsai,koren tattsai,Albasa da carrot,spring onions,sai ki rage wutan
- 3
Ki barsu su soyu sosai,bayan kin soyasu sai ki dauko ruwan nama kadan ki zuba bayan kin zuba sai ki kwaba cornflour da ruwa kadan sai ki zuba don miyar tayi kauri dan daidai kafun ki zuba dankalin,ki rage wutan don dankalin ya samu ya nuna.Bayan ya nuna sai ki sauke ki zuba kazan da kika soya a ciki shikenan potato soup naki is ready.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai