Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki samu tukunya ki zuba madarar seh ki zuba ruwan akai ki juya sosai ya zama ba gudaji,seh ki dora a wuta ya tafasa kina juyawa akai akai.
- 2
Idan ya dan tafasa seh ki sauke ki barshi ya huce dai dai yadda zaki iya sa yatsa ki dan barshi ba tare da zafin ya hana ki barin yatsar a ciki ba,wato dai yayi dumi amma ba sanyi ba.Seh ki kawo kindirmo ko yoghurt ki zuba a ciki ki juya sannan ki samu roba meh murfi ki juye a ciki ki rufe da murfin robar.
- 3
Seh ki rufe da kitchen towel ki saka a waje meh dumi ya samu Kamar awa 5 zuwa 8,seh ki duba ko yayi kauri idan beyi ba seh ki Kara barin shi.Seh ki saka a fridge saboda ya Kara kauri.seh ki zuba sikari idan kina so ki juya.
- 4
Gashi yoghurt dinmu ya hadu seh Sha.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12728274














sharhai