Shredded beef sauce da couscous

#couscous.Ina son couscous sosai saboda Yana da saukin dafawa,abinci neh da zaka hada shi cikin Dan kankanin lokaci.
Shredded beef sauce da couscous
#couscous.Ina son couscous sosai saboda Yana da saukin dafawa,abinci neh da zaka hada shi cikin Dan kankanin lokaci.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki zuba naman ki a roba ki zuba kayan hadin da na lissafa na marinade ki juya sosai ko ina ya samu seh ki rufe ki sa a fridge ya samu kamar awa daya.Daman kin riga kin yayyanka su carrot dinki duka kiyi musu yankan tsaye.
- 2
Ki dora pan dinki a wuta seh ki zuba mai kadan ki zuba naman,idan ya dan kame seh ki zuba albasa,dandano da kayan kanshi ki dan zuba ruwa ki juya ki barshi ya dan sulala,sannan ki kawo vegetables dinki ki zuba ki juya ya dan Samu minti biyu.
- 3
Seh ki dama corn flour da dan ruwa kadan ki zuba don yayi kauri,idan yayi Kamar minti biyu seh ki kara gishiri idan da bukata ki sauke.
- 4
Seh ki dafa couscous dinki,ki samu tukunya ki zuba ruwan seh ki zuba Mai Kamar chokali biyu a cikin ruwan ki sa dan gishiri kadan da Maggi ki zuba turmeric seh ki barshi ya tafasa,idan ya tafasa seh ki zuba sweet corn dinki da peas(nayi amfani da na gwangwani)seh ki rika zuba couscous din kadan kadan kina juyawa ya hade da ruwan seh ki rufe da foil ki sa murfin tukunya ki rufe ki kashe wutar ki barshi yayi Kamar minti shabiyar seh ki sa fork ki barbazashi seh ki kwashe.
- 5
Tip: idan zaki dafa couscous ana so ki sa ruwan daidai adadin couscous din zeh yi wara wara kuma ba zeh chabe ba.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes














sharhai (2)
kuma kin mana bayani dalla dalla 🤗