Jollop din wheat semolina pasta (Macaroni)

Inada sauran miyar da nayi jiya,kayan ya rage,na rasa mezanyi da ita,kawai sai nayi tunanin nayi amfani da ita nadafa Macaroni
Jollop din wheat semolina pasta (Macaroni)
Inada sauran miyar da nayi jiya,kayan ya rage,na rasa mezanyi da ita,kawai sai nayi tunanin nayi amfani da ita nadafa Macaroni
Umarnin dafa abinci
- 1
Wayennan sune kayan da nayi amfani dasu waje dafa wannan Macaroni
- 2
Abu nafarko,zaki dora tukunya kan wuta, saiki zuba mai da albasa kadan,idan yadanyi zafi,saiki zuba danyen nama aciki kinayi kina jujjuya shi,zakiga ya fara soyuwa
- 3
Saiki zuba tarugu da tattasai wanda kika yanka,sai kuma ki zuba sauran miyarki da kika rage saiki motsa
- 4
Saiki zuba ruwa iya dai dai yanda zai isa,sai kuma ki zuba maggi da sauran kayan dandano,zaki rufe tukunyar tatafasa
- 5
Bayan ta tafaso,saiki zuba Macaroni din aciki ki motsa saiki rufe yayita daduwa har yayi iya laushin da kike bukata
- 6
Idan ta kusa dahuwa,saiki saka albasar da kika slice dinta asama,ki rife,yadan dahu kadan saiki sauke
- 7
Shikenan kizuba aplate acikin😋😋
- 8
Keywords
Similar Recipes
More Recipes















sharhai (2)