Indomie pizza
Yana da dadi sosai😋😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan bukata,da farko zaki samu bowl dinki mai kyau ki fasa kwan ki a ciki kisa onga,curry, Maggi,da garlic sai ki dakko yankakken albasa da attaruhun ki ki zuba ki juya shi.(note:idan kin tashi dafa indomie din maginta kadai zaki sa ki dafa ta half done sai ki tsane ta kwalanda ruwan ya fita dan ba a so ta kasance da ruwa a jikin ta).
- 2
Sai ki dakko non stick dinki ko fry pan kisa mai bada yawa ba ki zuba rabin kwan ki aciki sai ki dakko daffafiyar indomie dinki ki zuba aciki ki bazata yadda kwan zai shiga jikinta sai ki juye raguwar kwan naki aciki ki gyara shi sosai ki rufe kasan ya soyu,bayan kasan ya soyu sai ki samu plate mai kyau kisa a saman non stick din sai ki juya shi aciki zai zama kasan da ya soyu zai zamana a sama kamar yadda yake a hotan kasa👇👇.
- 3
Sai ki sake mayar dashi cikin non stick din amma saman da bai soyu ba shine zai zamana a kasa kamar haka👇sai ki rufe shi shima ya soyu sai ki sauke zaki iya yankawa kamar yankan pizza sai aci😋😋.(abinda yasa bansa cokali nayi fliping din shi ba shine gudun kar ya ruguje idan kuma zaki iya amfani da cokalin batare daya ruguje ba zaki iya amfani dashi).
- 4
Done.....serve and enjoy with hot tea or drinks.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes












sharhai