Gasasshen naman rago(tsire)

Tsire daya daga cikin abincin siyarwa na hanya ne da ahalina suke matuqar qauna(a taqaice dai duk wani nama😂)to an zo da nama ne da yawa da za ayi amfani ni da yar uwata a dakin girki tace gsky ya kamata ayi gashi,ni kuma nace biryani za ayi ta dage qarshe na sakar mata,ga sakamakon hkn a gabanku😁❤

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a samu naman rago a gyarashi a yayyankashi yayi falen falen,a zuba garin cumin,rosemary, kimba,attaruhu da vinegar a cakudeshi da kyau,sai a rufeshi a ajiye cikin na'urar sanyi na tsahon awa daya da rabi
- 2
Sai a gefe guda a samu garin quli,a cakudeshi da garin yaji,sinadarin dandano da dan gishiri,sai a dauko naman a riqa mishi birgima cikin hadin qulin yabi jikinshi sosai,har sai an gama duka
- 3
Sai a dauko tsinkayen tsire a riqa soka naman a jiki,idan aka saka naman,sai albasa,sai jan tattasai snn koren tattasai,haka za ayi ta maimaitawa har a qare duka
- 4
Sai a samu farantin gashi a shimfida foil paper a shafeshi da mai a dora tsinkayen a kai,a qara bin samansu da wani man,sai a sakashi cikin na'urar yin gashin(za a iya amfani da double pan)
- 5
A gasashi da wutar sama ka 200°c,in bangare dsya yayi a qara juyawa dayan har a gama duka,shi knn.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (2)