Jollof shinkafa da wake

Inason abinci da ake sosai , kuma iyalina suma sunaso saboda haka mun ji dadin wanan girki
Jollof shinkafa da wake
Inason abinci da ake sosai , kuma iyalina suma sunaso saboda haka mun ji dadin wanan girki
Umarnin dafa abinci
- 1
Za,a gyara wake a cike daddin,a wanke shi tas a daura a wuta asa maggi daua da albasa a barshi ya tausa kamar minti 10, yadanganta da uadda tayi taushi kardai ta cika dahuwa ne, sai a juye a basket.
- 2
Sai a yi parboil na shinkafa itama a juye a basket.
- 3
Sai a dora tukunya a kan wuta, a zuba mai a soya mai da albasa,sai a soya kayan miya hade da da kakken diyar miya, sai a zuba ruwa yadda zai isa sai a dauraye waken a zuba a cikin tukunyar, a zuba maggi da kayan kamshi,da nama wanda akan dafa da ruwan naman a zuba.
- 4
Sai a barshi ya tausa, sai a zuba shinkafa a barshi ya dahu, sai ayanka albasa a ajiye agefe.
- 5
Idan ya kusa tsotsewa ya rage saura ruwa kadan,yadda ana ganin shinkafar ruwa bai rufe ta ba,sai a zuba curry da albasa akai kar a juya,sai a barshi ya tsotse a rage wutan.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai (2)