Wayna da miyar taushe

hadiza said lawan @cook_14446590
abincinmu na gargajiya karma da safe akwai Darin Karin kumallo #repyourstate.
Wayna da miyar taushe
abincinmu na gargajiya karma da safe akwai Darin Karin kumallo #repyourstate.
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko nawanke shinkafata saina Nika na dora ruwan dimi na kwaba yeast dashi sannan nazuba sai na rufe nabarshi ya tashi sannan nasa baking powder,kanwa ungurnu kadan,sugar najuya sosai sannan nasoya shikenan sai chi.
- 2
Sannan nawanke nama da tantakwashi nadora awuta nayanka albasa, kabewa kanana itama nazuba nasa gishiri,dan magi kayan kanshi tafarnuwa narufe nabarshi yadahu sannan nasa kayan Miya da mai da gyada na juyasu narufe nabarsu suka dahu sosai sai karshen nasa alaiyaju magi,kayan kanshi Kori kadan na rufe zuwa kamar minti biyar nasauke shikenan sai chi.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/14715039






sharhai (2)