Wainar fulawa

A kowane lokaci akwai abinci kala kala da muka tashi muka gani so yanayi yana canzawa muna kara kayatar da abinci mu wanan ne yasa na samu damar canza yanayin yin wainar fulawa kuma tayi dadi sosai

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki zuba fulawa a roba ki kawo maggi ki zuba da sauran kayan dandanon ki
- 2
Bayan nan sai ki kawo ruwa ki kwaba kamar dai yanda kuka san ana kwabin wainar fulawa sai ku aje gefe
- 3
Bayan nan sai ku dauko tandar wainar ku daura akan wuta sai ku bari ya fara zafi sanan ku kawo mai ku zuba kadan a cikin tandar sau ku zuba kullin wainar
- 4
Zaku barshi ne ya soyu gefe daya idan gegen dayan yayi sai ku juya dayan ma ya soyu ku barta ta soyu saboda cikin
- 5
Bayan nan idan tayi sai ku kwashe haka zakuyi har ku gama sai saka yaji harda albasa da tumatur idan kuna so
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (7)