Waina/ masa

Waina Yana daya daga cikin abincin gargajiya a kasar hausa, sainan kuma abun marmarine akoda yaushe, nakanyi waina kowace jumma'ah.
Waina/ masa
Waina Yana daya daga cikin abincin gargajiya a kasar hausa, sainan kuma abun marmarine akoda yaushe, nakanyi waina kowace jumma'ah.
Umarnin dafa abinci
- 1
Ajika shinkafar tuwo abarta ta kwana, da safe a wanketa a dafa na tuwo ahadasu wuri daya, sannan akai a niko, kada tayi tsululu ko kuma tayi kauri tsakatsaki akeso.
- 2
Azuba yeast, baking powder, gishiri da siga a motse ko ina yaji, sannan asamu wuri mai dumi ko kuma asa arana harya tashi, sannan a yanka albasa asa aciki, sai a daura tanda a wuta azuba mangyada.
- 3
Idan yayi zafi sai arika zuba kullu, idan gefe daya yayi sai ajuya dayan gefen, idan yayi a kwashe.
- 4
Ana iya cinsa da kuli kuli ko siga ko kuma da miya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes












sharhai (9)