Kunun Yamri/Dambu
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaa debi garin kunu kamar Kofi 3 sai ki zuba a roba kina saka ruwa kadan kadan ki na dama shi kina jujjuya robar don ya dunkule yayi curi curi
- 2
A jika gyada a bare bawon bayan a Kai nika ko a nika a blender a tace da rariya me laushi
- 3
A Dora ruwa Dan daidai a wuta in ya tafasa sai a zuba wannan garin da aka cura a saka bulugari ko fork a motsa a barshi ya dahu sai a kawo tatacciyar gyadan a zuba a Kai a gauraya sosai
- 4
A matse lemon tsami a zuba akai in yayi kauri a sauke asaka sugar asha.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/15771301















sharhai (4)