Turkish bread na alkama
Inason amfani da alkama saboda healthy eating.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki zuba gishiri da sukari da yeast cikin garin alkamarki sannan ki juya,seh ki zuba yoghurt,mai da ruwa ki kwaba ya hade jikin sa.
- 2
Sannan seh ki shafa mai a jikin shi kadan ki rufe ki barshi ya tashi.
- 3
Bayan ya tashi seh kiyi kneading ki rabashi gida 4 ko 5 seh ki rufe su ki barsu suyi resting tsawon minti10.Seh ki dauki daya ki fadada da hannun ki seh kiyi rolling da fadi da rolling pin.
- 4
Haka zakiyi wa sauran duka ki fadada su amma ki rufe wanda kika fara da kitchen cloth kar su bushe seh ki gasa a frying pan idan ya fara bubbles seh ki juya daya gefen seh ki shafa butter a duka sides din yayin da yake da dumin sa.
- 5
Haka za kiyi wa sauran har ki gama,ana iya ci da pepper soup ko kiyi mishi sauce da dankali a ci dadi lafiya.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes


















sharhai (4)