Juice din tsamiya da citta

Hauwa'u Aliyu Danyaya @Hawwer01
Juice din tsamiya da citta
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki fara daka kanunfari cikin turmi,sannan ki tsaftace cittar ki,ki saka ta acikin turmi da daka ta tare da wannan kanunfarin naki,sannan ki zube su a cikin roba,sei ki wanke tsamiyar ki da ruwan zafi ki zuba ta a cikin wannan robar sei ki zuba ruwa sannan ki barsu su jika
- 2
Idan suka jika sei ki sa hannun ki me tsafta ki murje wannan tsamiyar sannan ki kara ruwa kadan sei ki tace shi da matankadi
- 3
Idan kika tace shi da matankadi sei ki zuba sugar ki motsa shi sosae sannan ki sake tace shi
- 4
Sannan ki sa shi a fridge yayi sanyi.sei sha😂
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/15861882












sharhai (3)