Dambun Shinkafa mai Alaiyahu da lawashi

Dambun Shinkafa mai Alaiyahu da lawashi
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko na jika shinkafa tsawon awa 6, nawanke nabarbada gishiri
- 2
Nazuba a wankekken buhuna
- 3
Nadaura tukunyata a wuta da ruwa yar kadan, nasaka marfin tukunya a Kasan tukunyar yanda ruwan bazai haura saman murfin ba
- 4
Nakawo buhun da shinkafar me ciki nasaka akan murfin dake shikin wannan tukunyar narufe tukunyata, nasa wuta yar dedai
- 5
Yanayi INA Dan jujjuyawa da fork INA Dan daga buhun nakara ruwa akasa har yayi
- 6
Tiririn ya dafashi najuye a babban mazubi nasaka jajjagen tarugu yankakken albasa, mai, maggi, kayan kamshi da kuma Alaiyahu da lawashi na jujjuya har suka hade
- 7
Namaida cikin buhun NASA atukunya tiriri ya dan bugashi kadan nasauke nayi serving nayi garnishing da yankakken tomatoes da albasa da kuma siyayyar nama, mai gida da yara sukaci sukayi santi 😋😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes








sharhai (4)