Umarnin dafa abinci
- 1
A fere doya a wanke a dafa idan ta dahu se a daka a tirmi asa attarugu shima dakake
- 2
Asa kifi soyaye ko tafasashe a cire qaya asa kayan qanshi da sinadaran dandano
- 3
A hada a juya sosai ya hade se a mulmula kamar kwallo.
- 4
Se asamu flour da kwai a Fasa asa dandano da citta a kada shi se a dakko doyar da aka mulmula asa acikin flour
- 5
Se a ciro asa a Kwai a dora mai a wuta ye zafi a soya😋😋😋
- 6
Shikenan Akwai dadi sosai.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16226366







sharhai (3)