Ogbono soup
Nafee's kitchen
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaki jika ogbono ɗinki da manja ki ajje a rana, sannan ki dakko tukunyarki, ki dora akan wuta ki zuba ruwa sannan ki dakko namanki ki zuba dama tun farko kin sulala sa yadda ake so,
- 2
Sai ki dakko daddawarki da kika daka ki zuba tare da kayan miyarki, albasa, attaruhu,tafarnuwa.
- 3
Da sauransu duk sai ki zuba aciki, sannan ki rufe ta suyi ta dahuwa zuwa lokacin da kika gane sun dahu.
- 4
Sannan ki dakko kayan spices din ki ki zuba. Sannan ki dakko ogbono ɗinki da kika hada da manja sai ki zubasu
- 5
Sannan ki dakko kubewarki da kika gurza ki zuba aciki tare da ugunki, suyita dahuwa har zuwa lokacin da kikasan yayi sai ki sauke.
- 6
Tuwo zaki iya yin duk wanda kike so amma Ni da na shinkafa nayi. Kuma ina yin da na semovita. Aci dadi lafiya
- 7
Ki juya yadda ya maki. Sannan ki rufe ki barshi yadahu, dama can kin zuba roasted fish dinki bayan kin jika sa da ruwan zafi,
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





sharhai