Kosai mai kubewa
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko za'a jika waken na kamar minti biyu,sai a zuba a turmi a surfa shi,sai a wanke a cire duka hancin waken, a gyara kayan miya,sai a nika.
- 2
A buga kullin sosai yadda zai tashi amman kar yayi ruwa don zai sha mai ko ya kwanta,sai a kawo Maggi,gishiri,da garin kubewar a zuba,a qara bugawa sosai.
- 3
Sai a Dora mai a wuta,asa albasa,in yayi zabi sai ana diban kullin ana zubawa,in bari daya yayi sai a juya dayan barin ma, in yayi sai a kwashe.ga dadi ga ba Shan mai.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16319023




sharhai (5)