Dambun Nama
Dambun Nama Yana da Dadi sosai. Iyalaina sunji dadin sa.
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki yanka Nama kisa ruwa isashshe Sai ki zuba jajjage,spices da Maggi Sai ki rufe ki barshi yayi ta dahuwa yayi Kamar 2-3 hrs Yana dahuwa.
- 2
Bayan ya dahu ya tsotse ruwa gaba daya Sai ki sauke,Dama kin Riga kin wanke tirminki kin tsane Sai ki zuba Nama kina dakawa Idan ya daku Sai ki zube a tray kisa hannu ki Kara ware Shi.
- 3
Sai ki zuba Mai isashshe a pan ki zuba Naman Sai ki soya Shi a medium heat kiyi ta juyawa har Sai ya soyu
- 4
Bayan kin cireshi Sai ki Samu kyalle me kyau ki juye Naman ciki Sai ki kulle kisa cikin colendar Sai ki Aza dutse ko Wani abu me nauyi Sai ki barshi ya tsane sannan ki zube a tray ki warwareshi kada ya dunkule.
- 5
Shikenan dambunki yayi.
Aci Lafia😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16385597

















sharhai (3)
masha Allah😋