Dafa dukan shinkafa
To yau ance ranar jollof ce ta duniya..
#worldjollofday
Umarnin dafa abinci
- 1
Farko zaa gyara kayan miya a markada su a soya tare da tumaturin leda,
- 2
Sai a zuba ruwa da dandano da gishiri, idan ya tafasa a wanke shinkafa a zuba,
- 3
Idan ta tafasa a zuba kayan kamshi a rufe har ta dahu sai a sauke
- 4
Sai a wanke kayan lambu a yanka su kanana a ajiye gefe
- 5
A gyara kifi a wanke shi tas a soya a ajiye gefe
- 6
Sai a hada a Inda zaa ci, a Dan samu ruwa ko lemo a hada dashi
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16447660




sharhai (2)