Miyar kubewa bussashe

nayi wannan girkin ne saboda yara suna son miyar kuma suna tuwon da yawa duk lokacin da aka yi musu irinta
Miyar kubewa bussashe
nayi wannan girkin ne saboda yara suna son miyar kuma suna tuwon da yawa duk lokacin da aka yi musu irinta
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na fara da gyara kayan jajjage na wankesu sannan na jajjag
- 2
Bayanan sai na na daura tukunya a wuta na zuba mai na yanka albasa
- 3
Bayan albasa ya fara soyuwa sai na dauko gassashen nama na zuba cikin man saboda yadan soyu sama sama
- 4
Bayan ya dan suyo na tsame shi a wani mazubi
- 5
Sannan na zuba jajjage cikin mai na soya
- 6
Bayan kayan miyan ya soyu sai na rage shi cikin nama saboda banson kayan miyan ya bace ciki
- 7
Sannan banson naman ya watse ciki
- 8
Sannan nayi sanwa cikin sauran kayan miyan ba zuba magi star da fari da kuma onga
- 9
Sannan na zuba daddawa da kayan yaji
- 10
Sai kuma curry spices da gishiri
- 11
Na bar yy ta tafasa saboda miyan ya nuna da kyau sai da na kwatanci ruwan miyan ya rage sai na zuba sauran soyayyun kayan miyana da nama da albasa
- 12
Na barshi isuwa nuna sannan na kada miyan
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




















sharhai