Miyar kayan lambu

Na san ba ni na fara yin irin miyar nan ba, amma dalilina na qirqirarshi a kan kaina saboda Babana ne, yana son cous cous da miyar kayan lambu, alayyahu ne ko dai ko wane irin ganye, to wannan miyar dominshi na yi musamman.
Maganar gaskiya kuma sinadarin dandano da na yi amfani da shi a wannan miyar ita ce zan ce kusan sirrin fito da dandanon wnn miyar, mun ci miyar tare da dafaffen cous cous.

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a yayyanka kayan lambu fasalin da ake so, Sai a zuba mai cikin tukunya a daura kan wuta in ya yi zafi a zuba albasa ana juyawa zuwa minti daya da rabi sai a juye niqaqqen attaruhu da citta da tafarnuwa a siya na minti biyu,
- 2
Sai a kawo tumatur a zuba a saka sinadarin dandano a juya sai kuma soyayyar kaza
- 3
A zuba curry a juya, bayan mintuna biyar sai a zuba karas da yalo
- 4
Sai a zuba ruwan nama a dama corn flour da ruwa cokali daya a zuba, a zuba cauliflower da aka yayyanka aka wanke
- 5
Sai a zuba tattasai tare da kabeji a juya a rufe bayan an yi qasa da wuta na tsahon minti biyar sai a kashe wuta. Shi kenan.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (7)