Miyar rama da gyada

Salamatu Labaran
Salamatu Labaran @Salma76

Girkin miyar gargajiya ne saga Biu Borno.

Miyar rama da gyada

Girkin miyar gargajiya ne saga Biu Borno.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1hr
2 yawan abinchi
  1. Ganyen rama
  2. Kayan miya,
  3. Ruwa
  4. Gyada
  5. Gishiri
  6. Kayan kamshi da dandanon miya
  7. Manja
  8. Nama ko wake in ya samu

Umarnin dafa abinci

1hr
  1. 1

    Da farko zaa gyara rama a yanka kanana a wanke a tsameshi a ajiye a rife.

  2. 2

    A gyara kayan miya tsab a markada ko jajjaga a zuba a tukunya.

  3. 3

    A daka gyada a ajoyeshi.

  4. 4

    Sannan sai a tafasa idan da hali in kuma babu zaa iya sa wake.

  5. 5

    Bayan nan sai a dora kayan miya asa manja a dan soya saan nan a kawo kayan kamshi da na miya azuba a da ruwa daidai sanwa a rufe.

  6. 6

    Daga bisani in ya tafasa sai a zuba rama,a zuba gyadan a rude har ya hadu yayi kauri.

  7. 7

    Idan tsamin ya danyi yawa sai a dan sa kanwa don rage tsamin.

  8. 8

    Zaa iya ci da ko wani irin tuwo.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Salamatu Labaran
rannar
Am a journalist,love to cook every time.
Kara karantawa

Similar Recipes