Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki jiga shinkafan ki ya kwana a cikin ruwa sai ki dauko dafaffiyar farar shinkafa ki zuba akai sannan ki markada
- 2
Bayan kin markada sai ki saka yeast ki juya sai ki barshi a rana na tsawon 3hours ya tashi
In ya tashi sai ki juya ki zuba surgar ki zuba baking powder sai ki juya sannan ki dora tanda dinki a kan wuta ki zuba mai
- 3
Bayan mai yayi zafi sai ki zuba qullin a ciki bayan kin tabbatar ya soyu ciki da waje sai ki juya daya side din sai ki kwashe
- 4
Zaki iya ci da kuli za kuma ki iya ci da miyar taushe
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16505154











sharhai (4)