Meat pie
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farka zaki fara da tankade flour a bowl sai ki zuba butter, baking powder, madara,sugar,sai kiyi mixing dinsu da kyau
- 2
Daga nan sai ki fara kwanki guda daya ki zuba ruwa mai sanyi ki kwaba dashi.
- 3
Daga nan saikisa a fridge
- 4
For the filling kuma. Daman kin Riga da kin nika namarki sai ki samo tukunyarki kisa a wuta tareda mai, albasa, garlick da ginger sai ki dan soyasu sama sama
- 5
Daga nan sai ki zuba nikakken naman ki soyashi.
- 6
Sai ki zuba ruwa ki zuba Kayan dandanen ki da kikeson.
- 7
Idan kinason zaki iya dafa dankalinki da carrot daban idan naman tayi sai ki zuba akai ki gauraya. Idan kinaso kuma zaki iya zuba su veggies din tare da naman su nuna tare
- 8
Daga nan sai ki zuba su attarugunki ki chakuda da kyau. Anan sai ki kwaba cornflour dinki da dan ruwa ki zuba akai
- 9
Daman kin Riga da kin yayyanka koren tattarenki da ganyen albasa da dan scent leave to sai ki zuba akai. Hmmmmmmm wannan hadin ko ba a cewa komai sai ka gwada
- 10
Kinga yadda filling dinmu ya kasance
- 11
Daga nan sai ki fitar da dough dinki daga fridge Daman filling din na yayi sanyi sai kiyi rolling dinshi
- 12
Saiki zuba hadin akan cutter din
- 13
Sai ki shafa flour ko egg a bakin kamar haka
- 14
Sai ki rufe bakin ki yanka sauran dough na bakin
- 15
Gashinan mun gama. Ji yadda yayi kyau a ido
- 16
Sai ki jera a baking tray.
- 17
Sai kiyi egg wash dinshi
- 18
Sai ayi baking
- 19
Har sai yayi color da kikeson. Idan Ina meat pie ina egg wash sai biyu ko uku. Kafin nasa a oven zanyi idan ya fara gasuwa zanyi kam na kunna wutan sama shima zanyi wannan shine stirring baking dina🤩
- 20
Dan Allah kiga meat pie din nan
- 21
Gashinan bayan na gama baking kam
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



















sharhai (35)