Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki tankade fulawarki, ki saka gishiri da sugar da baking powder.
- 2
Sai ki saka butter Mai sanyi sosai, ki motsa ko'ina y hade, sai ki fasa kwai 1 ki saka.ki hade sosai.
- 3
Sai ki zuba ruwa Mai sanyi ki kwaba meat pie dinki, sai ki saka dough din a leda ki saka fridge yy sanyi.
- 4
Sai ki tafasa namanki, ki nikashi, koh ki daka, ki dafa Irish dinki, ki yanka kanana
- 5
Sai kiyi grating karas, tarugu da albasa, sai ki aje gefe.
- 6
Sai ki daura Mai a fan, ki saka albasa y soyu, ki saka thyme, sai ki juye karas dinki ki soyashi sama Sama.
- 7
Sai ki zuba tarugu da albasa, ki cigaba da soyawa, ki saka dandano da curry, sai ki juye namanki da kika niqa, da Irish, ki motsa, su hade ko'ina.
- 8
Sai ki kada corn flour da ruwa,ki juye aciki, sai ki rufe, y Dan tsotse.
- 9
Sai ki sauke, y Sha iska.
- 10
Sai ki dauko dough dinki a fridge, ki qara mulqashi, sai ki gutsura, kiyi rolling dinshi, sai ki saka meat pie cutter ki fidda shape din.
- 11
Ki saka filling dinki, sai ki shafa kwai at d edges, sai ki rufe, koh ki saka fork kiyi sealing.
- 12
Sai ki jera a baking tray. sai ki shafe, Saman meat pie din da kwai, sai ki gasa a oven.
- 13
Wutan sama da qasa.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai (2)