Soyayyiyar shinkafa da lemon mangwaro

#nazabiinyigirki
Wannan girki na yishi ne wa Yayata wadda nake bi, lokacin tana da juna biyu ta ce tana kwadayin fried rice, ta ji dadinshi sosai dan har yanzu lokaci lokaci tana ce min tana son qara cin irinta.
Abin takaicin dai 😫, yana daya daga cikin girkunan da na dauki hotunansu Daki daki daga farko har qarshe amma yanzu na rasa su sanadiyar lalacewar sdcard dina, 😥abinda ya sa jikina yin sanyi knn na ji duk daura girkin ma ya fita a kaina sbd na fi son saka cikakken recipe da hotuna. Yanzu dai haka zan daurasu ko ba cikakken ba tunda suna da yawa☹

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a wanke shinkafa da kyau a tafasa tare da star anise na minti 15, sai a tace.
- 2
A kasko mai fadi a zuba mai in ya dan fara zafi a zuba nama da aka wanke a soya na minti biyar,sai a zuba albasa a kai a soya sama sama
- 3
Sai a zuba kayan lambu ana juyawa,sai a zuba kayan qamshi a qara soyawa na minti biyu, a zuba sinadarin dandano
- 4
Sai a kawo shinkafar da aka tafasa a zuba a cakudeshi duka ana cigaba da juyawa a qara soyawa na minti uku, sai a yi qasa da wuta sosai a rufe a barshi ya qara turaruwa, shi knn an gama da shinkafa. Na qawata saman shinkafa da qwai soyayye da dafaffe
- 5
Lemon kuma za a yayyanka mangwaro a zuba cikin blender da qanqara da dan ruwa a niqa har yy laushi, sai a juye lemon soda a ciki a cakude. Shi knn.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (2)