Yamarita
Gaskiya naji daɗi ta sosai, gashi ko kadan bata shan mai🤩🤤
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fere doya ki wanke, ki dora ruwa a wuta sai ki zuba doyar kisa gishiri kadan sai barta Minti 5 ta dahu
- 2
Ki zuba a gwagwa ki tsayaye ruwan. Ki fasa kwai ki yanka albasa kisa sinadaran dandano sai ki motsa.
- 3
Fulawa ma kisa mata sinadaran dandano
- 4
Sannan ki sake sawa a kwai kisa a fulawai, haka zakiyi har ki gama
- 5
Sai kisa doyar cikin kwai sannan kisa a fulawa ki lullubeta da fulawar
- 6
Sai ki dora mai a wuta ki soya. Enjoy 😉
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16556669






sharhai (3)